1253 - (م) عَنْ ثَوْبَانَ قَالَ: كَانَ رَسُولُ الله صلّى الله عليه وسلّم، إِذَا انْصَرَفَ مِنْ صَلاَتِهِ، اسْتَغْفَرَ ثَلاَثاً، وَقَالَ: (اللَّهُمَّ! أَنْتَ السَّلاَمُ وَمِنْكَ السَّلاَمُ، تَبَارَكْتَ ذَا الجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ) .
Saga Sauban -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah SAW ya kasance idan ya yi Salama daga Sallarsa yana Istigfari sau uku: kuma ya ce: "Ya ubangiji kaine Aminci daga gareka aminci ya kr, Albarkatunka sun yawaita, ya Ma'abocin girma da Girmamawa"
[م591]