85 - عَن ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ: كُنْتُ خَلْفَ رَسُولِ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم يَوْماً فَقَالَ: (يَا غُلاَمُ، إِنِّي أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ، احْفَظِ اللهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إِذَا سَألْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الْأُمَّةَ لَوْ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَنْفَعُوكَ إِلاَّ بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ لَكَ، وَلَوْ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَضُرُّوكَ إِلاَّ بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ عَلَيْكَ، رُفِعَتِ الْأَقْلاَمُ وَجَفَّتِ الصُّحُفُ) .
Daga Abdullahi Dan Abbas zuwa ga Annabi "Ka kiyaye, Allah sai Allah ya kiyaye ka, ka kiyaye Allah Sai ka same shi duk halin da kasamu kanka, kuma idan zaka roki wani abu to ka roki Allah, kuma idan zaka nemi taimako to ka nemi taimakon Allah kuma kasani cewa da Al'umma zasu taru kan su amfanar da kai wani abu bazasu iya amfanar da kai da komai sai dai da abinda Allah ya rubuta maka shi, kuma da ace zasu taru da niyyar su cutar da kai to bazasu iya cutar dakai da komai ba sai da abinda Allah ya rubuta maka, kuma a dage Alkalami kuma takardun sun bushe, a wata riwayar kuma: "Ka kiyaye Allah Sai ka same shi a duk inda ka dosa, kuma ka tuna Allah lokacin kake cikin wadata sai ya tuna da kai lokacin da ka shiga tsanani, kuma kasani cewa duk abinda ya kuskureka daman cewa to ba'a rubuta zai sameka ba, kuma duk abinda ya sameka daman can rubuta zai same ka, kuma cewa lallai Nasara tana tare da Mai hakuri, kuma yayewar bakin ciki na tare da mai bakin cikin, kuma lallai cewa sauki na tafe bayan tsanani"
قال تعالى: {وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ}. [الحديد:4]
[ت2516]