Daga Jabir Dan Abdullah -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin Annabawa a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya gabanin haduwar mu, kuma aka sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah na kuma abar yin tsarki,don haka duk wanda salla ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , Ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane gaba daya
Mun fifita a kan mutane da uku: Ka sanya layukanmu kamar na mala'iku, kuma ka sanya duniya ta zama masallaci gare mu, kuma ka sanya mana kasarta tsarkakakke, idan ba mu sami ruwa ba.