An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa wani balaraben kauye yazo sai ya ce: ya Manzon Allah, "Lallai cewa matata ta haifi Bakin Yaro, sai Annabi ya ce Kana da Rakuma? sai ya ce E, sai ya ce yaya launukansu yake? sai yace: jajaye sai yace shin cikinta akwai wadanda yasha banban da su? ya ce: E lallai cikinsu akwai wadanda suka sha baban, ya ce: to ta yaya aka samu hakan? ya ce: To watakila ya gado jini ne, yace wannan ma watakila ya ya gado jini ne"
Daga Aisha Allah ya yarda da ita- tace: "Saad Dan Abi Wakkas sun yi fada da shi da Abdu Bin Zam'ata game da wani yaro: Sa'ad yace: Ya Manzon Allah wannan Dan'uwa na ne Utbata Dan Abi Wakkas, ya yi daawar cewa yaron nan dansa ne, kalli kamanninsa.sai Abdu Dan Zam'ata yace: ya Manzon Allah wannan Dan'uwana ne,an haife shi akan shimfidar Baba na ne yana daga 'ya'yansa.sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kalli kamanninsa sai yaga kamanceceniya da Utbata a fili, sai yace: Danka ne ya kai Abdu Dan Zam'ata, Da na uwarsa ne, kwarto kuma sai dutse,ki nesance shi ke Saudatu.Daga nan bai kuma ganin Saudatu ba".
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa Manzon Allah ya shigo wurina yana cikin farin ciki fuskarsa haske, sai ya c: "Baka ga Mujazzar ba dazu ya kalli Zaid Bn Harisah da Usama Bn Zaid, sai ya ce: Lallai wadan kafafuwa sunyi kama da juna" a cikin wata riwayar kuma da lafazin: "Ya kasance Mujazzar Masanin Nasaba"
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya ce: "Abu biyu acikin Mutane su daga sune kafircin sukar nasaba,da kukan kera abisa mamaci"