An karbo daga Abu Sa'id da Abu Huraira -Allah ya yarda da su- zuwa ga Anabi- Babu wani Musulmi da wata Wahala zata Same shi, ko rashin lafiya, Ko Damuwa ko Bacin rai, ko wata Cuta ko Damuwa, kai Har Kaya da zai taka ta face sai allah ya Kankare masa Zunubansa da ita
An Rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- daga Annabi cewa Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana gaida wasu daga cikin Iyalansa yana shafar su da Hannun Dama kuma yana cewa: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"
An rawaito daga Sauban -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Lallai Musulmi idan ya gaida Dan Uwansa Musulmi yana cikin fukakukan Al-jannah har sai ya dawo, aka ce ya manzon Allah Me nene Khurfar Al-jannah? ya ce: Fukafukanta"
An rawaito daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya yaje duba Mara lafiya wanda ajalibsa bai yi ba, sai ya ce: sau bakwai a wurinsa: Ina rokon Allah Mai girma, Ubangijin al-arshi mai girma, ya baka lafiya, sai Allah ya bashi lafiya daga wannan cutar"