الكِتَابُ الأوَّل: البيوع

قال تعالى: {وَأَحَلَّ اللَّهُ الْبَيْعَ وَحَرَّمَ الرِّبَا}. [البقرة:275]

2985 - (ق) عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم يَقُولُ: (الْحَلاَلُ بَيِّنٌ [1] ، وَالْحَرَامُ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا مُشبَّهَاتٌ لاَ يَعْلَمُهَا كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقى المُشَبَّهَاتِ اسْتَبْرَأَ [2] لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ، وَمَنْ وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ: كَرَاعٍ يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى [3] ، يُوشِكُ أَنْ يُوَاقِعَهُ. أَلاَ وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمىً، أَلاَ إِنَّ حِمَى اللهِ فِي أَرْضِهِ مَحَارمُهُ، أَلاَ وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً: إِذَا صَلَحَتْ صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ فَسَدَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، أَلاَ وَهِيَ الْقَلْبُ) .

Daga Nu'aman Dan Bashir -Allah ya yarda da shi- ya ce Naji Manzon Allah yana ewa: "Lallai Halak a bayyane yake, Lallai kuma Haram a bayyane ya ke, kuma a tsakaninsu akawai abubuwa Masu rikitarwa mafi yawan Mutane basu sansu ba, to duk wanda ya gujewa abubuwa masu rikitarwa to hakika ya kubutar da Addininsa da Mutuncinsa, kuma duk wanda ya fada cikin Haram, kamar mai kiwo ne da ya ke kiwo a gefen Gona ya kusa ya fada da Dabbobin sa ciki, ku saurara cewa kowane Sarki yana da Makiyaya, kuma cewa Makiyayar Allah abun da ya haramta, Ku saura ku ji cewa a jikin Mutum akwai wata tsoka idan ta gyaru to jiki ya gyaru baki dayansa kuma idan ta baci to jiki ya baci baki dayansa ku saurara kuji wannan it ce Zuciya".

2990 - (خ) عَنِ الْمِقْدَامِ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم قَالَ: (مَا أَكَلَ أَحَدٌ طَعَاماً قَطُّ، خَيْراً مِنْ أَنْ يَأْكُلَ مِنْ عَمَلِ يَدِهِ، وَإِنَّ نَبِيَّ اللهِ دَاوُدَ عليه السلام كَانَ يَأْكُلُ مِنْ عَمَلِ يَدِهِ) .

A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Dawud - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya kasance yana cin abinci ne kawai daga aikin hannunsa." Kuma a kan al-Muqaddam bin Muad al-Muqaddam - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Babu wanda ya ci abinci ya fi cin abinci daga aikin hannunsa, kuma Annabin Allah Dawud - Allah ya yi masa salati - ya kasance yana ci daga aikin hannunsa." .