Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Idan ina da kwatankwacin zinare, da na yi farin ciki da cewa darare uku ba za su wuce ni ba alhali ina da wani abu daga ciki sai wani abu da nake bi bashi."
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- "Duk wanda ya ga ainahin kudinsa a wajen wani da ya tsiyace -ko wani Mutum- to shi ne mafi cancanta da shi ba wani ba"