Daga Nu'aman Dan Bashir ya ce: Babana yayi mun kyautar wani abu daga cikin kudinsa, sai Mahaifiyata Amrah 'Yar Rawahata ce: Ba an taba yarda ba har sai Annabi ya shaida sai Mahaifina ya tafi wajen Annabi don ya kafa shaida da kyautar da yayi mani, sai Annabi yace da shi ko kayi irin wannan kayutar ga sauran 'yayanka? sai yace AA sai ya ce: " kuji tsoron Allah kuma kuyi Adalci gaY'ayan ku, sai Mahaifina ya dawo, kuma ya fasa wannan kyautar" a cikin lafazin wata riwayar kuwa: "To ni kada kasanyayi sheda tunda haka ne; don ni bana shaida kan Zalunci" a cikin wani lafazin kuma: "Nemi shaidar wani ba ni ba"
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Mai fasa kyautarsa, kamar mai dawowa ne cikin Amansa" a cikin wani Lafazin kuma: "Domin wanda yake fasa sadakarsa: kamar Karenda yai amai kuma ya dawo yana lashe shi"
Daga Umar -Allah ya yarda da shi- yace:"Na bayar da wani doki sabo da Allah,sai wanda dokin ke wajensa ya wulakantar da shi,sai naso in sayi dokin,don ina ganin zai sayar da shi da araha,sai na tambayi Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi-?sai yace: kar ka siya,kada ka karbe abin da kayi sadaka da shi,koda kuwa dirhami daya zai sayar maka da shi,don kuwa mai karbar kyautar da yayi,kamar mai yin amai ya lashe ne.".