Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Duk wanda ya 'yanda rabonsa na Bawan da sukai tarayya a cikinsa kuma yana da kuxin da zai iya cika ragowar kuxin sai a lissafa masa sauran rabon sauran ya biya don bawan ya 'yantu"
An rawaito daga Abu Musa Al-ash'ary -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Mutane Uku suna da Lada biyu: wani Mutum daga cikin Ahlul-Kitab da yayi Imani da Annabinsa, kuma yayi Imani da Annabi Muhammad, da kuma Bawan da ya bada Hakkin Allah da Hakkin Mai gidansa, da Kuma Mutumin da ya ke da baiwa ya kyautata tarbiyantar da ita, kuma ya sanar da ita kuma ya kyautata Sanar da ita, sannan ya Yantata sannan kuma ya Aureta, to yana da lada biyu"
Daga Ibn Umar - Allah ya yarda da su - ta hanyar isnadi: “Idan bawa ya yi wa ubangijinsa nasiha da kyakkyawar addu’a ga Allah, to za a ba shi lada biyu”. Daga Abu Musa al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - tare da isnadi mai yaduwa: "Sarkin da ya inganta bautar Ubangijinsa kuma yake kaiwa ga maigidansa wanda yake da hakki, nasiha da biyayya, yana da lada biyu."