An karbo daga Abdullahi Bn Mas'ud-Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Ya Allah kamar yadda na kyautata halaye na, haka kuma na kyautata halaye nai"
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : " Duk wanda yai Imani da Allah da Ranar lahira to ya fadi Alkairi ko yayi shiru, kuma duk wanda yayi Imani da Allah da Ranar Lahira to ta girmama Makwabcinsa,kuma duk wanda yayi Imani da Allah da Ranar Lahira to ta girmama to ya girmama Bakonsa"
Daga Abu Huraira zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya yayewa Mumini wani Bakin ciki na daga bakin cikin Duniya to Allah zai yaye Masa bakin cikin lahira, kuma duk wanda ya yalwatawa wanda yake cikinMatsuwa to Allah zai yalwata Masa a Duniya da Lahira, kuma duk wanda ya Suturta wani Musulmi to Allah zai Suturtashi a Duniya da Lahira, kuma duk wanda ya suturta Mumini to Allah shima zai Suturtashi a ranarDuniya da lahira, kuma Allah yana taimakon bawa Matukar Bawa yana taimakon Dan'uwansa, kuma duk wanda ya kama wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah zai sawwake masa hanyar shiga Aljanna, kuma Mutane basu taru ba a daki daga cikin dakunan Allah suna karanta littafin Allah sai Allah ya saukar musu da Nutsuwa akansu, kuma Rahama ta lullubesu, kuma Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah ya Ambace su cikin wadanda suke tare da shi, kuma duk wanda ya duk aikin da Dakire shi to Nasabarsa bazata sa yayi gaba ba.
Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - SAW- ya ce: "Allah mai girma da daukaka yana cewa a ranar kiyama: Ya ɗan Adam, shin ba ka na yi rashin lafiya ba amma baka duba ni ba?!, Ya ce: yaUbangiji ta yaya zan dubaka bayan kaine Ubangijin Talikai? amma ka san cewa bawana wane ba shida lafiya baka duba shi ba, Da ace ka gaida shi da ka same ni a wajensa ina tare da shi! Ya kai Dan Adam na nemi ka ciyar da ni ! Ya ce: Ya Ubangiji, ta yaya ka ciyar da kai kuma kai ne Ubangijin talikai?! Ya ce: Bakasan cewa Bawa na Wane ya bukaci a ciyar da shi ba amma baka ciyar da shi ba da ace ka ciyar da shi da ka same ni a wajensa,Ya kai Dan Adam na nemi ka Shayar da ni Ruwa amma ka ki! Ya ce: Ya Ubangiji, ta yaya zan shayar da kai Ruwa kuma kai Ubangijin talikai?! Ya ce: "Bawana Wane ya nemi ka shayae da shi Ruwa amma ba ka Shayae da shi ba, baka sani ba cewa da ka shayar da shi da ka samu ladan wancan a wajena"
An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Babu wata Dukiya da ta taba tawaya saboda Sadaka, Kuma wani abu da Allah yake Karawa Bawa da Rangwame sai Daukaka, kuma babu wani daya da zai Kaskantar da kansa ga Allah face Allah Madaukakin sarki ya daukaka shi."