Daga Anas bin Malik, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: ((Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, kuma ni da wani yaro muna dauke da na'urar ruwa da akuya, kuma zai yi tanadi da ruwa)).
An rawaito daga Katada Al-ansari -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Kada dayanku ya kuskura ya taba Azzakarinsa da Damansa, a halin yana Futsari kuma kada yayi tsarki, ko kuma yayi Nunfashi a Kwarya"
An karbo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - an daga shi zuwa g Annabi: 'kar waninku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi" A wata ruwayar: 'kar waninku ya yi wanka da ruwan da ba ya gudan alhali yana da janaba"
Daga Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya yarda s da shi yace: (Na kasance mutum mai yawan yin mazi, sai naji kunyar tambayar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi saboda matsayin y'arsa a waje na, sai na uamrci Mikdad Dan Aswad, ya tambaye shi, sai Annabi yace: Ya wanke Azzakarinsa, ya yi alwalla A wata ruwayar ta Buhari ((wanke Azzakarinka ka yi alwalla)) A wata ruwaya ta Muslim (( yi alwalla ka wanke gabanka))
Daga Abu Ayyub -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "dan kuka je yin bayan gida, to kada ku kuskura ku Fuskanci Al'kibla da Bayan gida ko Bawali, kuma kada ku juya mata baya, sai dai ku fuskanci Gabas ko kuma Yamma" Abu Ayyub ya ce cewa yayin da suka je Birnin Sham lokacin bude ta sun samiu a cikinta Bandakuna da akayi don biyan bukata an gina su suna kallon suna kallon Ka'aba, to Sun kasance suna karkacewa Alkibla, kuma sai suyi ta Istigfari