1 ـ باب: إِذا عرض بنفي الولد

Hadith No.: 2518

2518 - (ق) عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ: أَنَّ أَعْرَابِيّاً أَتَى رَسُولَ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم فَقَالَ: إِنَّ امْرَأَتِي وَلَدَتْ غُلاَماً أَسْوَدَ، وَإِنِّي أَنْكَرْتُهُ، فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم: (هَلْ لَكَ مِنْ إِبِلٍ) ؟ قَالَ: نَعَمْ، قَالَ: (فَمَا أَلْوَانُهَا) ، قالَ: حُمْرٌ، قَالَ: (هَلْ فِيهَا مِنْ أَورَقَ [1] ) ؟ قَالَ: إِنَّ فِيهَا لَوُرْقاً، قالَ: (فَأَنَّى تُرَى ذلِكَ جَاءَهَا) ؟ قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، عِرْقٌ [2] نَزَعَهَا، قَالَ: (وَلَعلَّ هَذَا عِرْقٌ نَزَعَهُ) . وَلَمْ يُرَخِّصْ لَهُ في الاِنْتِفَاءِ مِنْهُ.

An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa wani balaraben kauye yazo sai ya ce: ya Manzon Allah, "Lallai cewa matata ta haifi Bakin Yaro, sai Annabi ya ce Kana da Rakuma? sai ya ce E, sai ya ce yaya launukansu yake? sai yace: jajaye sai yace shin cikinta akwai wadanda yasha banban da su? ya ce: E lallai cikinsu akwai wadanda suka sha baban, ya ce: to ta yaya aka samu hakan? ya ce: To watakila ya gado jini ne, yace wannan ma watakila ya ya gado jini ne"

[خ7314 (5305)/ م1500]