2 ـ باب: الولد للفراش

Hadith No.: 2520

2520 - (ق) عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ: اخْتَصَمَ سَعْدُ بْنُ أَبِي وَقَّاصٍ وعَبْدُ بْنُ زَمْعَةَ في غُلاَمٍ، فَقَالَ سَعْدٌ: هذَا يَا رَسُولَ اللهِ ابْنُ أَخِي عُتْبَةَ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ، عَهِدَ إِلَيَّ أَنَّهُ ابْنُهُ، انْظُرْ إِلَى شَبَهِهِ. وَقَالَ عَبْدُ بْنُ زَمْعَةَ: هَذَا أَخِي يَا رَسُولَ اللهِ، وُلِدَ عَلَى فِرَاشِ أَبِي مِنْ وَلِيدَتِهِ، فَنَظَرَ رَسُولُ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم إِلى شَبَهِهِ فَرَأَى شَبَهاً بَيِّناً بِعُتْبَةَ، فَقَالَ: (هُوَ لَكَ يَا عَبْدُ، الْوَلَدُ لِلْفِرَاشِ وَلِلْعَاهِرِ الحَجَرُ، وَاحْتَجِبِي مِنْهُ يَا سَوْدَةُ بِنْتَ زَمْعَةَ) . فَلَمْ تَرَهُ سَوْدَةُ قَطُّ.

Daga Aisha Allah ya yarda da ita- tace: "Saad Dan Abi Wakkas sun yi fada da shi da Abdu Bin Zam'ata game da wani yaro: Sa'ad yace: Ya Manzon Allah wannan Dan'uwa na ne Utbata Dan Abi Wakkas, ya yi daawar cewa yaron nan dansa ne, kalli kamanninsa.sai Abdu Dan Zam'ata yace: ya Manzon Allah wannan Dan'uwana ne,an haife shi akan shimfidar Baba na ne yana daga 'ya'yansa.sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kalli kamanninsa sai yaga kamanceceniya da Utbata a fili, sai yace: Danka ne ya kai Abdu Dan Zam'ata, Da na uwarsa ne, kwarto kuma sai dutse,ki nesance shi ke Saudatu.Daga nan bai kuma ganin Saudatu ba".

[خ2218 (2053)/ م1457]