2522 - (ق) عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: إِنَّ رَسُولَ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم دَخَلَ عَلَيَّ مَسْرُوراً، تَبْرُقُ أَسَارِيرُ وَجْهِهِ [1] فَقَالَ: (أَلَمْ تَرَيْ أَنَّ مُجَزِّزاً [2] نَظَرَ آنِفاً [3] إِلى زَيْدِ بْنِ حارِثَةَ وَأُسَامَةَ بْنِ زَيْدٍ، فَقَالَ: إِنَّ هذِهِ الأَقْدَامَ بَعْضُهَا مِنْ بَعْضٍ) .
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa Manzon Allah ya shigo wurina yana cikin farin ciki fuskarsa haske, sai ya c: "Baka ga Mujazzar ba dazu ya kalli Zaid Bn Harisah da Usama Bn Zaid, sai ya ce: Lallai wadan kafafuwa sunyi kama da juna" a cikin wata riwayar kuma da lafazin: "Ya kasance Mujazzar Masanin Nasaba"
[خ6770 (3555)/ م1459]