3246 - (ق) عَنْ عائِشَةَ رضي الله عنها: أَنَّ قُرَيْشاً أَهَمَّهُمْ شَأْنُ المَرْأَةِ الْمَخْزُومِيَّةِ الَّتِي سَرَقَتْ، فَقَالُوا: وَمَنْ يُكَلِّمُ فِيهَا رَسُولَ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم؟ فَقَالُوا: وَمَنْ يَجْتَرِئُ عَلَيْهِ إِلاَّ أُسَامَةُ بْنُ زَيْدٍ، حِبُّ رَسُولِ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم؟ فَكَلَّمَهُ أُسَامَةُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صلّى الله عليه وسلّم: (أَتَشْفَعُ في حَدٍّ مِنْ حُدُودِ اللهِ) ؟ ثُمَّ قامَ فَاخْتَطَبَ، ثُمَّ قَالَ: (إِنَّمَا أَهْلَكَ الَّذِينَ قَبْلَكُمْ، أَنَّهُمْ كانُوا إِذَا سَرَقَ فِيهِمُ الشَّرِيفُ تَرَكُوهُ، وَإِذَا سَرَقَ فِيهِمُ الضَّعِيفُ أَقامُوا عَلَيْهِ الحَدَّ. وَايْمُ اللهِ، لَوْ أَنَّ فـاطِـمَـةَ بِـنْـتَ مُـحَـمَّـدٍ سَـرَقَـتْ لَـقَطَعْتُ يَدَهَا) .
Ankarbo daga A'isha-Allah ya yarda da ita-"Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu,sai suka ce:Waye zai yiwa Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi maganarta?,sai suka ce:Ba wanda zai iya tararsa sai Usama Dan Zaid Masoyin Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai Usama ya gaya masa,sai yace:ka nemi Ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah?sannan ya tashi yayi huduba,sai yace:Hakika abinda ya halakar da wadanda suke gabaninku cewa su sun kasance idan wani Mai'alfarma daga cikinsu yayi sata sai su rabu dashi,idan kuma Mairauni ne acikinsu yayi sata sai su tsayar da Hukunci akansa,na rantse da Allah:da cewa Fadima yar Muhammad za tayi sata da lallai na yanke Hannunta".Awata ruwayar kuma"Wata Mace ta kasance tana arar kaya sai kuma ta musashi,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi umarni da a yanke Hannunta"
[خ3475 (2648)/ م1688]